Fassran mafarkin Ruwan Teku

FASSARAN MAFARKI NA RUWAN TEKU Asslamu alaikum mafarkin kogi na nufin sarkine Ko mulki mai karfi.idan mai mafarkin dan kasuwane to wannan yawan kaddaransane, idan mai neman ilimine malamin sane idan mutum ma aikacine to wannan aikinsane. Ko wanne mai mafarki zai fahimci haka daga matsayin sa. Wanda yayi mafarki ruwan kogi ya taba wani Abu to tabbas mutum zai Sami abin. Idan mutum yaga ya nutse a cikin kogi Hakan na nuna zaiyi mu amala da masu mulki. Idan kuwa ya ganshi Yana taka doron ruwa Ko Yana konce a kansa, to zaiyi mu amala da masu sarauta amma zai kasance cikin hasari da Lili kuwa ba a amincewa da dulmuya cikin ruwa. Wadda yai mafarki yaga ya shan ye ruwan kogi gaba daya to zai mallake duniya sannan rayuwan sa zaiyi tsawo. Idan kuwa ya ga ya Shane ruwa har ya bar saura zai Sami arziki mai yawa sannan har ya mutum bazai iya cinyewa ba. Idan kuwa neman ya sha ruwan yake Hakan na nuna Yana neman aiki wajen masu mulkine. Idan kuwa mai mafarkin yaga ya ketare kogi to hakika zai ribace dukiyar makiyan sa. Idan kuwa aka ga lokin ya shiga wani gari makil sannan banyi masu barnaba Hakan na nuna samun arzikin Garin da yawa zai zo musu daga wata masarauta. Idan kuwa gani Ko hangen kogi kayi daga nesa samun alkhairi ne daga mai sarauta. Idan kuwa kayi mafarki kogin daga can nesa sosai to wannan wahala ce da fitina da fatara. Allah ya tsare.

Comments

Popular posts from this blog

Illoli da Magungunan Karfafa Aure ga Mata

MAGANIN MALLAKA

Gyaran Nono ga Mace: Maganin Gargajiya da Muhimmancinsa