Yadda ake wankan janaba,mukoyi ibada.
Asslamu alaikum warahmatullahi ta ala wabar katuhu, Ina mika gaisuwa Ga shugaban Halittu, sira da aminci su tabbata garesa tareda alayengidansa da sahabbansa , Annabi muhammadu sallalahu alaihi wasallam. Shine wadda yakawo Haske duniya waton ilimi wadda da wannan hasken muke gane yadda zamu fuskanci mahaliccinmu don yin ibada. JANABA yana daga cikin muhimman abubuwa da yakamata duk wani musulmi musamman baligi ko baliga susani. TAMBAYA: menene Janaba? AMSA; Janaba shine fitan maniyyi daga Al auran mace ko na miji a yayin saduwa ko mafarki ko makamantansa ko buyan kan azzari cikin farji. Janaba zai kama namiji da macen ko A yayinda maniyyi ya fito Janaba yasami mutum Ko kuma yayi taimama idan lalura ya samu kamar rashin ruwa ko sananin sanyi idan zai shutar. Shi Janaba yana kama namiji da mace kuma nauin wanka iri daya akeyi da niyya iri daya. Ya dace mutum ya iya wankan Janaba Dan inba laruriba sallah da Janaba baya halatta. Kuma duk ibada da aka aikata da jana ba ...