Yadda ake wankan janaba,mukoyi ibada.

Asslamu alaikum warahmatullahi ta ala wabar katuhu, Ina mika gaisuwa Ga shugaban Halittu, sira da aminci su tabbata garesa tareda alayengidansa da sahabbansa , Annabi muhammadu sallalahu alaihi wasallam. Shine wadda yakawo Haske duniya waton ilimi wadda da wannan hasken muke gane yadda zamu fuskanci mahaliccinmu don yin ibada. JANABA yana daga cikin muhimman abubuwa da yakamata duk wani musulmi musamman baligi ko baliga susani. TAMBAYA: menene Janaba? AMSA; Janaba shine fitan maniyyi daga Al auran mace ko na miji a yayin saduwa ko mafarki ko makamantansa ko buyan kan azzari cikin farji. Janaba zai kama namiji da macen ko A yayinda maniyyi ya fito Janaba yasami mutum Ko kuma yayi taimama idan lalura ya samu kamar rashin ruwa ko sananin sanyi idan zai shutar. Shi Janaba yana kama namiji da mace kuma nauin wanka iri daya akeyi da niyya iri daya. Ya dace mutum ya iya wankan Janaba Dan inba laruriba sallah da Janaba baya halatta. Kuma duk ibada da aka aikata da jana ba ba a karba. Allah mai tsarkine baya karban aikida datti.ko shekara nawa kayi kana sallah ba tareda kayi wannan Janaba ba aikin banza kayi, don haka iyan uwa yanada cikin ilimi daya dace mukoya kuma mukayar don kaucewaa asarar lahira. Wankan Janaba, ba wankanda yafishi sauki amma wasu basu saniba, to amma yau zanyi takaitaccen bayani yadda ake wankan Janaba ta yadda za a fahimta da wuri. Da Fari asamo ruwa mai tsabta a bokiti ko Buta ko wani abin da zai dauki ruwa. sai a je bayangida a tsuguna sai a wanke najasar dake gabanka, waton yin tsarki kenan.Bayan kammala haka saikayi alwaka Amma zaka wanke gabobinka sau daidai, bayan kammalla alwala sai ayi niyy a wanke gefen barin jikinka Na dama haka Na hagu duka daga saman kai har kasa sai shudanya jiki ko ina sai game jiki da ruwa. Amma idan mutum zaiyi wankan janaba kogi wannan basai yayi alwalaba. Abinda zaiyi shine zaiyi niyyaa azuciya ko a bayyane NAWAITUL GUSLULJANABATI. sai yayi mismillaha ya fada cikin ruwa ko kogi ya shuadanya jikinsa ya kare. In ba kogine ba ana bukatan ruwa ya taba ko INA a jiki.

Comments

Popular posts from this blog

Illoli da Magungunan Karfafa Aure ga Mata

MAGANIN MALLAKA

Gyaran Nono ga Mace: Maganin Gargajiya da Muhimmancinsa