Hasken rayuwa.
Aslamu alaikum iyan uwa inai muku fatan alkhairi , ina tafe da muhimmin bayani kan hasken tayuwa , menene hasken raayuwa? abinda nake nufi a wannan dan takaitaccen rubutun nawa shine hasken rayuwa shine ilimi , bazamu rayu in ba haske ba, dan da haske muke kallo muke rasa duhu ,muke kuma gane komai gorgodon iko , ilimi nada matukar muhimmanci a rayuwarmu don haka nake kara bamu shawari mudage da neman ilimi kukuma daure komai wuya. Abu mai amfani ba a samunsa cikin sauki, dalilin Wannan shawari shine ganin yadda matasanmu a yanzu da dama basu damuda neman ilimiba. Misalin abin kamar mutumne yana tafiya a cikin duhu bai kuma nemi haskeba wadda zai rika taimaka masa wajen ganin hanyar don kaucewa hadaruruka. Idan nuka duba da dama wadda suke fadawa wasu matsalolin rayuwa mai muni da dama wayadda basuda ilimine. Don haka zan takaita bayani haka . amma abinda zan rufe dashi shine. Mai karatu mu lura wannan zamani da muke ciki na masu karatune .duba da irin cigaba da kallum ke tunkar...